ALHAJI MUHMADU NAGODA:

YA RASU A 1965 YANA DA SHEKARA 78

     Ya fara saye da sayarwa tun 1908 ya zama babban d'an kasuwa sa'ad da a kejin labarinsa ko ina a cikin 1922, kuma shi ne d'an kasuwa na farko a nan Kano wanda ya fara sayen motar sufuri. Har ya rasu bai daina ba. Ya yi fatauce-fatauce tun ana tafiya kasa da kan jakuna, kuma yana daga cikin mutanen da suka jawo hankalin 'yan kasuwa dangina masakar (KCTC) wadda har yanzu ta na aiki kuma Alhaji Mudi Nagoda yana d'aya daga cikin Darektocin Kamfanin.
            Shi marigayi kuwa su ne masu sayen gyad'a na farko a nan kasar tun sa'adda ton na gyada ana sayensa 50 /- kuma ba kamasho, marigayi ya sha gwagwarmaya cikin sayen gyad'a tun wannan lokacin ba kamasho har aka zo ana ba da 2/6 har dai zuwa wannan zamani wanda ma kafin ya rasu sai da aka ba shi L. B. A. kuma Alhaji Mudi Nagoda yanzu shi ne ke rike da wannan L. B. A.
Alhaji Muhammadu Nagoda ya sha taimakawa wajen aikin hukuma da girmamata kuma shi nadadden Wakili da hukuma ta nad'a ne cikin Town Council. Yana daya daga cikin 'Yan Kasuwa da jama'a su ke girmamawa da yarda da irin shawarwarin da ya bayar ko ga hukuma ko ga jama'a. Ya bar 'ya'ya da dama wanda cikinsu Alhaji Mudi shi ke rike da Kamfanin har yanzu.