Alh Alhassan 'Dantata 
(1877 - 1952)

Source: Kano Jiya Da Yau.

Allah mai baiyana bayinsa ta irin yadda ya so cikin ikonsa, Sarki mai cikakken iko da babu kama tasa, Ubangijin Talikai masu kamannu daban-daban. Ka ba mu ikon bayyana takaitaccen tarihin wannan bawa naka domin da shi zan yi misali ga sauran jama'ar kasa don su koyi irin halayensa na kirki da girmama shugabanni, taimakon 'yan'uwa da rashin girman kai don Allah ba don riya ba, da rashin wulakanta bayin Allah wadanda ba su da wadata. 

    Wanda kowane mutum, in dai cikin Afirka ya ke ya ji sunansa in dai har an ambaci sha'anin kudi ko safara to, shi Allah ya fifita. Sai jama'a su ce "ko kai ne Alhassan Dantata mai kudi kamar yashin Binuwai na Kano." Don haka za mu kawo maku jerin wadansu masu safara na yau, ba wai don su kai kamar sa ba, sa'a ai wannan baiwa sai wanda Allah ya fifita. An ce shi Alhaji Alhassan shi ne ya gaji sunan wani Sadaukin Attajiri da aka taba yi a Kano wai shi Kundila. Wanda ake cewa ba na sayarwa ba ne shi ne kawai ya gagari Kundila. Ni Alhaji Muhammadu Nalado na yi hira da zuriyar jikan Kundila a Kano lokacin binciken wannan tarihi. Wannan hoton na tuna lokacin binciken tarihin Alhaji Alhassan 'Dantata, ga kujerarsa nan da 'ya'yansa a bayansa sun dare kujerar dama da hagu manyan 'yan kasuwar Kano ne wadanda ke da sauran rai wadanda suka yi zamani da sadaukin safara Alhaji Alhassan sauran na tsaye duk za ku ga guntun tarihinsu ko da yake ba mu son mu ba da tarihin mutum yana da rai a duniya, sai dai munyi wannan don niyyar gurimmu taimaka a samu safara na kirki da tsai da gaskiya ga matsalolinsu don 'ya'yammu da jikokimmu masu tasowa nan gaba. A littafin da ya shafi yankin yamma kuwa AIhaji Abdun Zagi shi ne sadaukin attajiri abin misali wanda aka yi shi a Sakata birnin Shehu Usman Danfodio Allah ya ba mu albarkacinsa amin amin.

Sarkin Musulmi Hassan Dan Mu'azu adalin Sarki abin misali na yankin yamma. Sarkin Kebbi Sarna da Sarkin Sudan Nagwamatse. Mayakan da suka tsare kasashensu a lokacin su. Malamta abin misali Abdullahin Gwandu. Yarda da juyin zamani Sarkin Gwandu Yahaya da Sarkin Musulmi Sir Abubakar Sarkin Musulmi na goma sha bakwai. Shugaban Musulunci, adalci da bayyana gaskiya na yankunan rukunin Arewa. Haton Alhaji Alhassan Dantata wanda aka haifa a Bebeji ta Kasar Kano a 1877 ya rasu a Kano cikin 1952 yana da shekara 75 a-duniya ya bar duniya cikin daraja ta daya a cikin fannin safara in da za ka ji takaitaccen tarihinsa na gaskiya da taimakon samun wadansu dasussa a rubuce kuma tsofafin da taimakon zuriyarsa a kan hakikanin gaskiya. Shi Alhaji Alhassan 'Dantata tun yana yaro, mutum ne mai ladabi da kwazo kuma an sa shi makaranta don Ubansa Malami ne. An ce shi malamin lokacin da yana ciwon ajali ya fada ma Amarya matarsa kuma ita ce tsofuwar Alhaji Alhassan'Dantata da mu ke magana. To, ga yara nan ki kula da su da kyau in Allah ya nufi ki gani to, don ki kula ba ni son ki yi sake ga su sami tarbiyya ta gari cikin su za a sami sadauki amma ko ni ban san kowanene shi ba sune: Alhaji Bala, AIhaji Alhassan, M. Jaji da Sidi Kaninsu.

Bayan rasuwar Malami ita amarya ta koma Accra don ita attajira ce tana cinikin hajja da goro ta aiko zuwa Kasar Hausa a saya mata shanu, shi Alhajl Alhassan da 'yan ubansa ya ci gaba da karatu da sana' a a Bebeji kuma duk suna da labarin juna don yakan tafi can wajenta ya dawo ta hanyar fatauci Yanzu haka asusun da Alhaji Alhassan ya fara tara kudi yana nan a Bebeji gidansu na can wurin ya zama gidan Tarihi nan ne ya tara kudin da ya fara fatauci da su. Duk da kudinsa na sana'a in ya je Accra wajen tsofuwarsa attajiran nan amarya, sai ta hana shi abinci ta ba shi koko ta ce ya shiga gari ya wo bara ai shi almajiri ne. Sai ya tafi ya wo ya ci ya zo da kudi da abinci, sai ta dauki kudin da abincm ta bayar sadaka, haka suka yi ta yi har wata rana ya je gidan wani attajiri Tanko Sarkin Yarabawan Accra bara, sai yaran attajirin suka fada masa cewa ai wannan saurayin dan aminiyarka ce Maduga Amarya ya zo daga kasar Hausa. Sarkin Yarabawa ya taso da fushi sai wajen Amarya ya ce: Yaya zaki sa’a wulakantamu ace dan mu ya zo kin bar shi ya yi bara, to, menene amfanin anikinki. In haka ne ni daga yau sai mu bata, don ko ke ba ki san iyakar kudin ki da jama'a suka halaka ba, to, d’a ai ba abin da ya fishi.Amarya tace wa Sarkin Yarabawa kada ka damu na san haka, kuma na san abin da na ke nufi, in ko ka ki to, sai dai mu bata. Allahu Akbar ita Amarya tana son ta gane ko shi ne ubansa ya yi mata wasici da shi don tana ganin wasu alamomi, ita ma tana zaton zai zama wani Shehun Malami ne.Haka yayi tayi har almajirai suka gane ga wani almajiri da ya ce, 'Allazi wahidun sai ya samu. Don haka almajirai suka yi ta binsa in ya yi bara duk sai su samu, in ya koma gida da abincin da kudin da ya samu har da sutura sai tsofuwarsa ta amsa ta rarraba ma sauran almajiran.

Har rannan Alhaji Alhassan ya ce ma tsofuwarsa ni kowa ya samu kudinsa sai ya ajiye ni ko sai ki bayar duk abin da na samu sadaka. To, ni yaushe zan tara kudi ko ba ki son in tara. Sai ta yi murmushi ta ce ai wannan da ka ga ina bayarwa duk kai a ke ma tariya in Allah ya so kai za ka girbi shukar da aka yi da irin da ka sarno, kuma ina sa ka bara, ba don ba ni son ka ba, sai don in jarraba wani al'amari da aka sanar da ni to, na kuwa tabbata kai ne. To, ina foronka da kame ka ke da shi ka inganta sadaka kome yawansa kome kankantarsa, lokacin duk da ka so ganina ka taho nan Accra yan kudinka da ka zo da su kayita juya abinka na sal1ameka kuma kada ka yarda ku rabu da 'yan'uwanka ko wane irin al'amari ya faru ku gama kanku.
Alhaji Alhassan ya wo 'yan saye sayen sa zai yi amfani ya shigo ta kwalekwale zuwa Lagos. Tun wannan lokaci ya ke ta safara ya sayo ya sayar, yana kuma rike da hanyar makaranta.

A Ebute Metta ne aka sace duk dukiyar da Alhaji Alhassan ya ke tare da ita bayan ya fito Acra yana tare da matarsa guda Hajiya Tsofuwar Alhaji Sanusi aka bar shi bashi da shi da kome a hannunsa. Nan ebute Metta ya sayar da alkur’aninsa (sule 30) ya bayar da sule gama sadaka to, sauran (sule 20) - da ta rage su ne asalin kudin Alhaji Alhassan Dantata, don da su ya yi tajuyawa ko da yake an san shi da sha'anin dukiya har suka yi yawa kwarai da gaske. Ya tafi. Acra ya je Lagos ya zo Kano da gida Bebeji. Yana cikin wadannan tafiye-tafiye ne Alhaji Alhassan Dantata ya fito Acra cikin jirgin ruwa za shi Lagos, sai ga wani tsofo yana sanye da fararen kaya ya ce ma Alhaji Alhassan kai samari, ina za ka, ya bayyana masa shi dan kasuwa ne za shi Lagos ya yi sayayya ya tafi .kasar Hausa. Sai tsofon ya ce to, amshi Alhassan ya durkusa ya amsa sai ya ga dutse irin wanda ake sayarwa a wasu kantuna. Tsofon ya ce to, in ka isa Lagos kada ka wuce Hausa ka nemi irin dutsen nan duk abin da ka mallaka ka sayo shi, ka koma Accra da shi za ka yi amfani da Allah kadai ya san iyakar al'amarin. Alhassan ya sa dutsen aljifu ko da ya daga kansa sai baiga tsofo ba. Nan ya yi Salla raka’a 2 ya yi godiya ga Ubangiji don haka da Alhaji ya isa Lagos ya sauka, sai ya yi ta bin kantuna da dan dutsensa a kulle a hankici yana duddubawa, har ya ga dutsen a kantin Iliyasu mai Kanti a Kantin Ferisgeoge. Ya dauko nashi dutsen ya duba ya ga sun yi daidai sai ya ce ina son irin dutsen can, Iliyasu ya ce guda nawa ? Alhassan ya ce duk ma nake so in saya. Iliyasu ya ce kai yaro ka yi karya duk Suton Ferisgeoge. Alhassan ya ce in dai bai fi kudina ba zan biya, in ya fi in sayi na iyakar kudina. Aka yi lissafin akwatan dutsen suka kama £1,200. Ya ce to, ina zuwa ya isa masaukinsa gidan Sarkin Fawa, ya zo da kudi suka yi ta mamaki ya auna dutse Accra ya koma da isarsa ya sayar da dutsen £10,000 to, tun wannan lokaci har zuwa yau dukiyar Alhaji Alhassan sha'anin sai Allah kuma har yau har go be dutsen da hankicin suna nan ga zuriar Alhaji Alhassan Dantata. An ce shi Al'amarin wannan ainihin dutsen na cikin hankici da Allah ya bayar da shi ga Alhaji Alhassan Dantata to, ni dai na yi shiru al'amarin Allah ya fi da haka.

Tun wannan lokaci ne su Ferisgeoge suka san Hausa akwai kudi Suka fara shirin tanadin aikowa don bude kanti a Kano inda Alhaji Alhassan ya fito don sun ga gaskiya. An ce su Ferisgeoge su suka fara kafa kanti a Kano yanzu sai 'ya'yansu da Jikokinsu, zuriyar Ferisgeoge Sune masu (Plaza cinema) a Kano da Katsina.

Alhaji Alhassan ya komo Kano da zama bayan mutuwar Tsofuwarsa Amarya dake Accra, alokacin Sarkin Kano Abbas, kafin sarkin Kano ya ba shi wurin da zai yi gida sai da ya zauna a Unguwoyi. A lokacin ne aka ba shi sarari wurin duk daji ne ita ce koki a yau, wanda har akan cika sunanta da koki unguwar Alhaji Alhassan Koki unguwar Alasawa don duk yankin daga diya sai jikoki da barori. Ko wane mitum ya samu wani wurin to, AIhaji Alhassan ya ba shi ko 'ya'yansa sai dai abin da ba a rasa ba.

Alhaji Alhassan 'Dantata arzikinsa ya wuce ace yana da gida kaza ko yana irin sana'a kaza don kusan ko wace kasa akwai yaransa da dukiyar da ya ke aikawa su kai su sayo. A wannan lokaci ya fi karfi ga goro da shanu sha'anin Lagos ban da sauran cike cike. Ance sau da yawa mutum zai zo daga wata kasa yana tambayar gidan Alhaji Alhassan don ya ganshi kawai, wasu kuma ko ya ce masu shi ne Alhaji Alhassan sai dai su ce to, amman ba don sun yarda ba. Don sun ga bai da girman kai ko nuna isa ga jama'a don yawan dukiyarsa. An ce har Alhaji Alhassan Allah ya yi masa rasuwa bai taba wuce riga uku ba. In ba wata to, ya bayar sadaka ya dinka wata, kuma ba riguna. Irin na riya ba. Girmama shugabanni Sarakuna da masu kudin Kano wanda ya iske ko da shi ke duk ya take su amman duk da haka in dai ya ga tsofon attajiri ko malami sai ya cire takalmansa su gaisa ya yi maka hassafi ba na riya ba, kuma yayi maka rakiya, Allahu Akbar malam ka ji sadaukin safara.

RASUWAR ALHAJI ALHASSAN

Bayan ya rasu aka raba gado mace da namiji kowa ya samu na shi, amman duk da haka suna nan had'e kuma Kamfanin na ci gaba karkashin Alhaji Ahmadu and Alhaji Sanusi. Sai cikin 1959 1okacin da aka raba Kamfanin biyu, Alhaji Ahmadu wanda shi ne Halifa a wannan lokaci ya mayar da ci gaba da sunan AD. and Son.  

SHA'ANIN GIDAN ALH.ALHASSAN

   Lokacin da mawalIafin wannan littafi (Kano Jiya Da Yau) ya ziyarci Halifa shugaban Alasawa Alhaji Sanusi'Dantata ya ce sha'anin gidan Alhaji alhassn dai kansu game shike don alhaji aminu shi ya gabatar da su zuwa ga halifa don samun wasu darussa da ke rubuce tun rayuwar alhaji alhassan. Cikinsu na taras kuma na tambayi halifa alhaji sanusi don in ji hakikanin gaskiya.

  Shi alhaji alhaji sanusi dantata tun 1937 ya sami kudi na kansa $15,000, jaka dari da hasin. Lokacin yana zaune a danbatta wadannan kudi ba kwabo guda na ubansa ciki. Don haka hankalinsa ya tashi ya zo kano wajen tsofonsa alhaji alhassan ya bayyana masa, cewa yana jin tsoro wai an ce in mutum bai wuce shekara 40 ba in kudi sun same shi ba shi yawancin rai.

   Alhaji ya yi murmushi yace, ba kome kada ka damu kayi ta kokari wannan maganar ba gaskiya ba ce, ai sanin abin da za’a yi gobe sai allah. Kai dai ka tsare ibada ka kuma yi ta yin sadaka ban da riya kowa ya saba ma ubangiji allah, komi ta gaba da sha’aninsa a danbatta. A wannan lokacin da na ke Magana a kansa to, malam ka ji yadda mazan jiya ke ma ‘ya’yansu gargadi.

   Lokacin ziyarar ne mawallafin ya tambayi alhaji sanusi shugaban alasawa cewa yau da safe an ce kasa ‘yam mata daya-daya har goma sha takwas lalle duk suna nan hannunka cinsu da shansu da kayan aurensu duk kai ke yi, shin wadannan ‘yam mata duk kai ka haufesu ? sai alhaji sanusi ya yi murmushi, y ace ko an ce ni na haifesu ai ko kai ka yi gardama. To, ga bayani in ji alhaji Sanusi Dantata “Tun lokacin maigida wannan al’ada take, don haka wanda duk ke babba shi ne zai dauki wadannan ayyuka kuma ‘yam matan ana bad a su ga wadanda suke so. Amma fa sai in mutanen kirki ne taron ‘yam maan daga diyan mud a diyan yarammu da barori da dangi duk suna hannuna kuma kome na yi shi ne daidai allah dai ya sa mu gama lafiya da ingata kowace hanya ta kirki a bias lalatacciya Amin.”

   Wannan shi ne hoton alhaji Sanusi Dantata shi ne halifa watau shugaban alasawa na kano. Bisa hakikanin gaskiya ba maganar sa gishiri ga labari sha’anin zuriyar alhaji Alhassan Dantata. Sai muce it ace Teku ga sha’anin safara ta kasashen nan, yadda duk zamani ya juya. Don in ka dubi irin dashen da Alhaji Dantata yayi, shuke shuken arziki  banda bizne to, ni dai mawallafin wannan littafi ina sanar da jama'a abu biyu. Wad'anda dubban jama'ar kasashemmu suka amince suka yi imani a kansu. Na farko dai muddin kasashen nan namu ana azumi ana sallah, girma abu ne na gargajiya da darajarsu ba ta fad'uwa. Na biyu muddin sha'anin safara na kasashen nan in dai da kud'i ake yinsa to, zuriyar Alasawa ta amshi gaba. Malamin na tsaya kawo maka dalilai d'aya d'aya na gaskiya tsintsa da tsinsa , wannan littafin da in an gama shi yaro mai shekara bakwai ba zai iya d'aukar sa ba ! ko lokaci ne na annabi shafo sai in dakata kan dalilai ka yi, aiki da hankalinka akan wad'annan abubuwa da na ambata. Wannan hoton Alhaji Aminu 'Dantata ne wanda ke tafiyadda Kamfanin A. D. & SONS. tun August 1960 in daya canji wansa marigayi Alhaji Ahmadu 'Dantata, ya kara karfin sha'anin Kamfanin fiye da da, wajen sufuri da kwangila gine-gine. Shi ya gina yankin Makarantar A. Bello University Zariya da Babban Asibitin Malumfashi da 'Danbatta. Wad'anda jimlar kud'in da aka biya shi fam miliyan d'aya da 'yan kai. Ma'aikata kuwa ba kabilar da ba ka samu cikin kamfanin Alasawa.

Source (Kano Jiya Da Yau).