ALH ABDULLAHI BAYERO

 Wazirin Kano ! Ciroman Kano ! 
Sannan kuma Sarkin Kano !

 

Sarki goma Zamani goma !!!
Tarihin sarauta a Kano ba zai cika ba, sai an hada da tarihin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, Shi ne Sarki na hamsin da uku daga lokacin da aka kafa Kano
AD 999 har ya zuwa sa'an da ya yi Sarki. Yin sarautar sa 1926, ya shafe wani tsohon chamfi a Kano, cewa Ciroman Kano, ba ya yin sarautar Kano. Bayan ubansa ya yi sarauta 1903, sai aka nada masa sarautar Wazircin Kano, Yana Wazirin ne, Rasdan na Kano na zamanin Mr. Cargill, ya ce Sarki ya ba shi Waziri-Abdullahi Bayero su yi rangadin kasar Kano. Kusan babu garin da ba su je ba ! suna duba arzikin kasa (Economic Survey). An ce a Gaya suka rubuta labarin aikinsu da suka gama. A wannan lokaci hakimai a cikin birni su ke a zaune, sai yaransu suke aikawa kauyuka su yiwo haraji da jangali. Wadannan irin yaran hakimai, su ake kira Jakadu. Irin harajin sa'an nan Shi ne kudin shuke, kudin karofi, jangali da zakka. Zakka ita ce karbar dami daya a ko wane dami goma na mutum. Abin da jakadu suka kawo wa Hakimi, shi za'a kai wa Sarki. A kan kasa shi uku, Sarki kashi d'aya Hakimai da jakadu da Dagatai kashi daya, kashi daya kuma a ajiye a Baitulmali don wasu lalurori.
Wannan rangadi da na ambata ta shi aka gane shirin hanyar
sarauta a Kano yana bukatar canji. Aka daina yin jakadu, aka yanyanka kasa, aka kai Hakimai. Wannan yanyanka kasa, Shi ake kira guduma aka yi wa Dr. Cargilll lakabi da "MAl GUNDUMA". Saboda haka akwai hannun Wazirin Kano Abdullahi Bayaro a cikin kafa hanyar mulkin nan da a ke kai yanzu, A rangadin na su har sun ketara kasar Katagum, saboda kara samun karfin shaidar abin da su ke so, su kafa. An ce Mr, C. L. Temple ya jarraba Wazirin Kano ya ga ko Waziri yana fahintar abin da su ke yi. Wani lokaci sai ya ce da Waziri yau je ka ka yi aiki, ka kawo mini. lrin yadda duk Baturen ya ke yi, haka Waziri ya ke yi. Har akwai masu zaton tun daga sa' an nan Turawa suka yaba hankalinsa suka ga wannan mutum Waziri Abdullahi Bayaro ya isa ragamar jan mutane hannunsa.

Turawa sun kai sun kawo a kan ko Dagatai za'a karfafa, ko Hakimai, amma wani mai hikima ya taimaka a kan a karfafa Hakimai. Saboda haka wajen rangadin nan, bar mai bangar Waziri sunansa Gara, a cikin waka, ya ce :
Kwanammu dari da biyar
Rabommu da matammu
Kai mu gida darman.
Daga baya aka canjawa Waziri sarauta, aka yi masa Ciroman Kano. Aka saka Hakimai goma a hannunsa, shi ne jagoran su akan kowane sha'ani na kasashensu, zuwa ga sarki. Wannan shiri yayi kama da Kancila, (COUNCILLOR) mai portfolio. A rayuwa tasa, a garuruwa biyu ya zauna yana Hakimi. Gidan Hakimin Dawakin Kudu shi aka ginawa, haka kuma na Bici inda ya dade, daga nan ne ya yi sarautar Kano. Wadanda suka fi ni hikima sun riga sun zama irin abubuwan da Kano ta samu na alheri a lokacin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayaro don haka ba zan maimaita ba.
Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero a ko yaushe ya kan ce fadi gaskiyar komi ban tsoron ta, karshen abin sai ya zama alheri. Wajen wannan yana koyawa jama'a su fadi gaskiya ko da a kan su ko 'ya'yansu ko makiyan su.
Wajen 1928, sa'ad da ya zo Makarantar Shahuci ya fahimci
babu yara daga mutanen Bakin Kasuwa, attajirai, sai 'ya'yan mutanen fada kawai. Saboda haka ya yi magana da Alhassan 'Dantata da kuma wasu Tajirai akan me ya sa ba su kawo 'ya' yan su makaranta ba. Sai suka ce su suna tsoron cudanya 'ya'yan su da 'ya'yan Saraki don kada 'ya'yan saraki su rika dukan su. Sai ya ce to, idan haka ne za'a yi maku makaranta daga can wajen gidajen ku don ku rika kai 'ya'yan ku. Sai aka gina Makarantar Dala, a gabas da Dala kadan.
     Wannan dabara ita ta budawa yaran Tajiraineman ilmin zamani. Ba don haka ba da za'a dade ba'a sami masu ilmin zamani ba a cikin 'ya'yan Tajirai. Sa'ad da aka gina Asibitin Shahuci a lokacin nan mutane ba su son zuwa Asibiti, hatta maza bare mata, a lokacin kuwa babu wasu 'Ya'diresa sai maza. Ana nan ana nan sai mutane suka fara gane amfanin Asibiti, to, amma sai abu guda ya tauyo zuwan su kamar yadda su ke so. Shi ne dubawar da 'yan diresa maza ke yi wa mata a wuri daya da maza. Da Sarkin ya fahimci haka sai ya sa aka kebe wajen mata dabam wajen maza daban, kuma aka yi kokarin neman 'Yandiresa mata don jinyar mata. Sai mutane suka yi ta zuwa ba ji ba gani. Haka kuma ya yi wajen shigar Dubagari gidaje. Ya sa aka sami mata masu shiga gidaje.
A lokacin Sarkin ne aka bude Majalisar Dagatai. Sa'ad da kararrakin barayi suka yi yawa a kauyuka, sai Sarki ya ba
Majalisar Dagatai izini a wurin shawara su rika ambaton sunayen barayin da su ke zaton su su ke yi masu sata. Aka rata wannan sai A1kalai suka rasa yadda za su tabbatad da laifi a kan irin wadannan da a ke tuhuma, domin in an kawo su gun Alk:ali sai makwabtansu, su ce ba su san suna sata ba amma suna fadi ne don tsoron in barawon an daure shi ya fito daga kurkuku kada ya cuce su. Sai Sarkin ya koya masu dabara ya ce, su rika tambayar mutanen K'asar da ke makwabtaka da su. Da barayi suka ga mutanen K'asar da ke makwabtaka da su suna zuwa suna bankadar asirin su, sai suka rika gudu.
Zuwan sa Hajji shi ya sa mutanen Kano da yawa, masu sarauta da ma'aikata suka rik:a kokarin zuwa Hajji akan motoci kafin a sami Jirgin Sama. Akwai dokoki da yawa wadanda ya yi a zamanin sa don amfanin jama'a. Wadansu akan kiyaye 1afiya, kamar dokar rikon Alade saboda gudun ciwon Jiga, dokar taryen kaji saboda hana tsadar kajin, dokar ayyuka masu hadari, irin su kona alIi, jima da sauran su, dokar kashin yawo don kiyaye ciyawa da tsire tsire masu amfani. Kusan a kowace harka ba wadda bai kafa doka ba don amfanin jama'a. Mutum ne mai tsinkaya matuka. Lokacin da aka kawo ruwan famfo a Kano, cikin 1931, an shawarce shi daya kamata abinne rijiyoyi na cikin birni domin a huta shan ruwa mai kazanta, tun da ga ruwan famfo mai tsabta kuma mai kyau. Har an soma cike rijiyoyin, amma sai ya ce a bari, kowa ya yi wa tasa kyaure ya rufe don 1a1ura.
A lokacin Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayaro aka soma yin bauca (VOUCHER) a Kano. Akwai wani Bature ana kiran sa Lt Commander John H. Carrow, an fi sanin sa da Mista Kara), a sa'an nan yana Mataimakin D.O. ya kawo shirin a rika yin bauca kafin a karbi kudi daga Gidan Ma'aji. Kafin sa'an nan sai Shugaban Ma'aikata ya dauki alkalamin kara, ya tsomo taddawa, ya rubutawa Ma'aji, "Ga wane nan, ka bashi albashin sa kaza, ni ne wane." Mai karatu, ka ji jiya. Yanzu haka za tayiwu? Yanzu ana "Na shaida na tabbata" ma yaya aka kare. Kuma a wannan lokacin ne aka shirya yin rasit (Receipt), aka shirya Peshi (pay-sheet) a da duk ba'a yi.

Kila mai karatu zai ce yaya ake biyan lebura a sa'an nan. Cikon hanya da birji fam guda ne ga kowane min can da farko. Hakimai da taimakon Sarkin Tafarki ko mataimakinsa, za su rubuto yawan min da suka aikata akan kowane daya fam daya, su aiko birni, a kai musu kudin. Lebura dai kudinsa taro ne ga kowane yini, ta haka za'a biya leburan. Ga kudi ko a hannun riga ko a faifai, a tsattsakura.

Babban halin Sarkin Kano Bayero da ya shahara da Shi, shi ne yi wa makiyi ahuwa. Wannan hali ne da akan samuga zababun mutane 'yan kadan. Shi aka samu an san tsakaninsa da wani mutum babu kyau, ran nan mutumin nan ya dauko ruwan dahuwar kansa, mutane su tabbata ko zai daure shi, ko zai masa wani abu irin na sakayya, amman sai a ga bai yi daya ba. Wannan ya yi daidai da yanda wani maroki, Dodo mai taushi ya yi masa waka:
"Sadauki gyara Rasa ta yi kyau Babba ka sami taimakon Allah."
Mutum ne mai lafiya ta jiki. Sai da ajali ya kusato shi, ya soma samun 'yan lalurorin rashin lafiya. Samun irinsa da wuya sai dai a kamanta, daidai ruwa, daidai Kurji.
To, Jama'ar yau da na gobe kunji cikakken Tarihin Adalin Sarkin Kano, wanda ko yaushe in ana tunanin irin ayyukansu nagari zai sa a samu masu koyi da su. Kuma kowane dan Adam ya yi adaki a sha'aninsa na zaman duniya to, ko bayan ransa.

Allah madaukakin Sarki zai bayyana bayansa. Don haka Sarkin Kano Alhaji Ado Bayaro ya yi tsaye nan yarda da juyin zamani. Jama'arsa birni da kauye sun amince da Kwazonsa, in dai har an ce Sarkin Kano ya ce to, duk jama'ar kasar sun san sha'anin zai zama alheri a garesu. Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero na daya daga cikin uwayen yankinmu jama'ar Nijeriya masu son a bayyana gaskiya, wadanda darajarsu da girmansu a cikin kasashenmu ba zai fadu ba har iyakar rayuwar kasar nan tamu ta yankunan Jihohin Arewa. Sai dai wadansu gyare gyare muddin dai ana azumi ana sallah, don an gina su ne ta tushen Musulunci da yin kowane sha'ani cikin adaki da shawara. Irin wadannan muhimman Sarakuna su ne ni Alhaji Mamman Nalado ni kan kira su da sunan Tsofuwar zuma da ku akan yi magani. (amma fa ban da rubaba) Allah shi taimakemu amin. Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wanda ya hau gadon sarautar Kano cikin shekarar 1963 dan Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero ne. Amma wanda ya gaji Alhaji Abdullahi Bayaro a bayan rasuwarsa shi ne Alhaji Muhammadu Sanusi wanda ya ke shi ma dan Alhaji Abdullahi Bayaro ne kuma Wa ya ke ga Alhaji Ado Bayero. Alhaji Muhammadu Sanusi ya yi shekara 10 yana mulkin Kano kafin ya yi murabus. A zamaninsa, an san shi akan kokarin shari'a da tsananta hukunci ga miyagun mutane masu hana sakewa-kamar barayi don gyaran kasa, sa'an nan kuma shi mai himma ne wajen yin Limanci a dukkan Sallar Jumma'a muddin yana gari.A bayan Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi sai Baffansa, Alhaji Muhammadu Inuwa Abbas wanda kuma ya ke Kanen Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ne, ya shiga gidan Dabo  amma bai jima ba sai rai ya yi halinsa domin ya rasu bayan wata shida da hawansa gadon sarauta.
Daga Sarkin Kano Inuwa Abbas sai Alhaji Ado Bayero ya gaje shi, ya shiga Gidan Sarautar Kano akan Sarkin Kano na 56 tun lokacin da aka kafa Kano cikin shekara ta AD. 999.

Kano wuri ne da ya dade yana yin sa' a ga dacen Sarakuna amma Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero yana daga cikin Sarakunan da Kano ba ta sarnu kamar su ba wanda ya ke kuma ya daidaita sosai da zamanin da Allah ya bashi ragamar jan jama'arsa. A cikin lokacin da ya hau gadon sarauta samun ilmi fanni biyu (watau ilmin arabiyya da na zamani) ya zama wajibi ga kowace harka. Akan haka kuwa za'a gane lallai Kano ta yi babban dace ga samun Sarki kamar Alhaji Ado Bayaro wanda ya ke mutum ne mai zurfin ilmi na kowane fanni. Idan ka juya ga ilmin muhammadiyya sai ka ce tamfar ba ya da na daya, in kuma ka komo ga ilmi irin na zamani sai ka ji tamfar nan ya fi aboki.
Ko kafin ya zama Sarkin Kano sai da ya yi wasu muhimman ayyuka inda ya nuna bajinta da Kwazo, ya kuma yi amfani da ilmin da Allah ya bashi. Da farko dai ya taba yin Wakilin Dokar Kano wanda har don saboda ganin Kwazonsa da himmarsa da dagewa akan gaskiya har Gwamnati ta zabe shi don ya wakilci Nijeriya, watau ya zama Jakadanta a K'asar Senegal. A cikin zamanin da ya yi yana wannan mawuyacin aiki na Jakadanci, ya nuna basira da hikima, ya kuma yi amfani da zurfin ilmin sa wajen hulda da K'asashen Waje wanda ya jawo masa Kauna da farin jini a Gida da K'asashen Waje, ya kuma jawowa Nijeriya kwarjini da martaba ga idanun duniya.

Source (Kano Jiya Da Yau).