ALHAJI GARBA BICHI:


               An haifi Alhaji Garba a Bichi ta K'asar Kano. Shi Alhaji Garba dan Malam Ali ne; wani sanannen dan kasuwa na Bichi. Alhaji Garba ya yi makarantar muhammadiya a Bichi kuma Malaman sa su ne Malam Bawa da Malam Umaru sa'an nan kuma ya iya rubutu da karatu na nasariya. A cikin shekara ta 1943 ya faa sha'anin saye da sayarwa tun yana da shekara 20 a duniya. A cikin 1945 ya fara sayen gyada domin Kamfanin London Kano da CFAO da John Holts Co. Ya ci gaba da wannan har cikin 1952, sa'an nan a cikin 1960 sai Alhaji Garba ya sami LB.A. don sayen amfanin gona. Shi kuwa yana daya daga cikin ‘yan kasuwa masu tafiyar da sha'anin su ba tare da tuhumar ha'inci ba.