ALHAJI HARUNA KASSIM (1917-1967)


   Ya fara aikin masinja a G.B.O. yana da shekara 20 in da ya yi shekara 2 kawai daga nan ya bari ya kama shop bayi bar shekara 2 inda daga nan ya bari ya kama ciniki da su yana daya daga cikin manyan 'yan kasuwar gidan, san nan ne ya tafi Makka cikin 1944 a mota shi ne bayan ya koma ya ga irin wahalar da mutane ke sha kan taftya Makka a mota don haka ya himmatu don shirya da yin tanadin a sami hanyar daukar mutane a jirgin sarna. Nijeriya Airways suka ce su ba za su dauki kowa ba amma duk da haka ya matsa suka dauki mutum 4 Kawai shi ma zuwa Khartum Kawai. 1946 ne ya sarno mutum 25 ya kai musu suka ce sai su biya 260 kowane mutum, suka biya aka dauke su a dan kararnin jirgi zuwa Jidda inda sai da suka sauka kamar sau 8 kafin su kai, wanda a wannan lokaci babu filin jirgin sarna sosai a Jidda sai cikin rairayi, suka sauka. 1947 ya nemo jirgin mutanen Aidan ana kiranshi jirgin York wanda suka yi kamar shekara 3. (J 950) yana daukar Alhazai. San nan 1952 yaje Congo yajawo SABENA in da a san nan can Headquarter su ta ke. Ya kawo su gun Mai Girma Sarkin Kano Alhaji Abudullahi Bayero, ko da yake a wannan shekara ba su yi da su ba, sai da ya koma ya sake nemo London Airwaysa cikin 1954 ne ya sake koma da su SABENA gaban Mai Girma Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sanusi in da suka yi yarjejeniya nan " gabansa na daukar Alhazai shi ne har ya zuwa yanzu. Duk da wannan harka ta Alhazai yana da abubuwa da dama na ciniki kamar su L B. A. ta sayen gyada tun kamar shekara 6, da tramport kamar shekara 14 da noma zamanin jahiliyya bar ma da na zamani da cinikin hajja kwanuka da sauransu.