Alh Nabegu:
(1892-1965)

 

 


 
An haifi Alhaji Nabegu a shekarar, 1892. An sa shi a makarantar Alkur'ani yana da shekara goma. Bayan ya sauke Alkur'ani. Sai ya shiga neman ilmin addini yana d'an shekara 22. Ya yi auren fari tun daga nan sai ya shiga harkokin kasuwanci. Yana sayen hajjoji kamar su alwayyo, akoko da atamfofi daga Kano, ya kai kauyuka domin sayarwa. Bayan shekaru kamar biyar yana haka, sai kuma ya ci gaba da zuwa, Lagos, da Ankara domin sayo goro yana kawowa nan, yana sayarwa. Bayan an sami kamar shekara goma yana haka, sai kuma ya daina zuwa, amma ya ci gaba da tura yaransa domin yi masa wannan ciniki.
        Sai ya maida hankalinsa gun cinikin fatu da kiraga da kuma cinikin gyad'a. Kamfunan da ya ke hurda da su game da wannan ciniki su ne: Wajen cinikin fatu da kiraga, shi ne L. Ambrosini Ltd. Wajen cinikin gyada kuma shi ne G. Olvant. Kuma yana ci gaba da harkokin kasuwancinsa da aka soma d'aukar Alhazai a Jirgin sama. Sai ya zama Wakili, lokacin da aikin ya ke hannun, Sabena. Bayan da Gwamnati ta baiwa 'yan kasa tasin na d'aukar Alhazai sai ya zama Wakilin Kamfanin AJhaji Haruna Kassim. Kuma shi yana cikm wakilcin Majalisar Wakilai ta Arewa har shekara kamar goma. Kuma har zuwa yanzu shi 'Dan Majalisar N.A. ta Kano ne. Ya rasu bayan tarihin 1968.