Alh Mai Sango Sarina.  
(1899-1967)

 


  
         Ya fara saye da sayarwa yana da shekara 18 a duniya wanda ya yi cinikin haja kuma ya yi tafiye, tafiye da dama cikin kasashe kan wannan ciniki, kuma yana yin noma kwarai. Kuma dukan kantuna na nan Kano yana daga cikin manyan 'yan kasuwa yana d'aya daga cikin wad'anda suka fara tafiya Makka a mota daga nan Kano (36 years), don bud'ewa jama'a ido na su dena wahalar tafiya a kasa. Kuma cikin wad'annan shekaru har zuwa yau kullum yana ba da goyon bayamsa ga hukuma kan dukkan abubuwan da ta nemi su sa hannu ko shiga ciki.
Har ma yana d'aya daga cikin mutanen da hukuma ta nad'a don shiga Majalisar Wakilai ta Birnin Kano.