Alh. Hassan Na Badamasi  
(1880- 19??)

 

Ya shiga saye da sayarwa tun yana da shekara 18 a duniya har zuwa 23 in da ya fara zuwa Lagos tahanyar barance, na wa- ni Bayarbe, Bello wanda ta haka ne, mu je mu kama, ni ma ta haka na ware na kama nawa cinikin Dutse, ina saye daga na Kano in kai Lagos kuma in sayo 'yan kaya ina komawa har zuwa shekara 9.

 

Sa'ad da Larabawa suka tabbata cewa mu 4 kadai muka san irin wannan ciniki don haka duk wanda suka kawo wa dutse daga kasashen India, sai Larabawa su neme mu mu saye duka shine a cikin 1907 na bude hanyar zuwa Onisha na irin wannan ciniki na dutse, Izgar Giwa da Jar fata har zuwa shekaru 40 in da na ban fasa sayarwa ba, kuma 'ya'yana su ne yanzu kan fatauce fatauce yanzum zuriya sun kai 70 haihuwata 58 mace da namiji. Kuma a Logos muna ciniki da kantin Ferisgeoge har ganin suna samun riba, suka zo nan Kano suka bude kanti da sharadin duk irin kayan da mu ke saye tun Lagos mu ne za su sayarwa da sauki don mun zama 'yan gida, Suka yarda suka biyo mu zuwa Kano,