ALHAJI BABA LATSU ALFINDIKI  (1895 - 1952)


   Alhaji Baba Latsu ya fara saye da sayarwa yana da shekara 20 da haifuwa, ya kuwa fara ta hanyar kayan koli tun ana tafiya Lagos a kasa kafin su fara shiga jirgin kasa daga llorin tun daga nan ne suka fara samun saukin tafiya har ma jirgi ya kawo Zariya inda nan ne ma suka mayar gun daffonsu.

   Baba Latsu, Alhaji Hassan Badamasi da Malam Sharubutu Koki da Alhaji Katin suka jawowa kuma su ne su 4 stika jawowa Kantin FIRJOJI hanya zuwa Kano ana kiran Kantin na su "YUSUFU HALILU KULLUHUN SAWA'UN" kuma dukkan Larabawa ko mutanen INDIYA masu sayar da dutse da alharini in sun zo ba su kaiwa kowa sai su domin a wannan lokaci babu wanda ka ke shiga cikin cinikin wani kuma shi wannan ciniki na KOLI shi ne wanda Alhaji Baba Latsu ya yi har ya mutu.
Alhaji Baba Latsu shi ne ya bude hanyar YAMAI ta cikin Faranshi ya na aikawa da yaransa su na kai kayan hajjoji iri iri su kuma suna sawo shanu daga can suna wucewa KUMASHI in sun sai da shanun a can sai su sayo GORO su komo nan Kano.
       Kuma Alhaji Baba Latsu shi na cikin wanda da suka fara bude tafiya Makka a jirgin ruwa a cikin 1926 inda suna can ne Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayaro ya zama Sarki.
A cikin 1928 nan ne ya zauna a zaune ba ya fita fatauci ya sanya 'ya'yansa su Alhaji Isiyaku da Alhaji Ahmadu suka bude cinikin goro zuwa Duwala suna kaiwa suna kawowa har lokacin daAlhaji Ahmadu ya bada sha'awar cewa ya kamata dayammu ya kama Duwala ya zauna shi ne cikin 1940 aka tura babban da shi ne Alhaji Isiyaku ya koma can da zama shi kuma Alhaji Labaran ya koma Kongo Kinshasha ya zauina, shi kuwa Alhaji Ahmadu Baba yana aika musu da kaya su kuma suna aikowa har zuwa 1952 in da shi Alhaji Baba Latsu ya rasu ya bar 'ya'ya 37, maza da mata.   Cikin kaiwa da kawowa na fatauci da 'ya'yansa suka yi, cikin 1941 AIhaji Ahmadu Baba ya tafi Malandabo da fatar Guza ta 8 ya sayar da ita 250 ya zauna nan har shekara guda yana saye yana sayarwa sannan ya koma Kano. Bayan ya shirya zai sake komawa Malandaho sai ya gamu da fatake a Port Harcourt suka ce masa cinikin Malanbaho ya lalace su tafi Duwala, da isarsu Duwala ya sayar da kayansa ninki uku na yadda ya sayo shi ta nan ne ya zauna har zuwa yau yana fataucin Duwala kuma wansa zuwa yar yana can. Alhaji Ahmadu Baba yana ciniki iri iri bar ma yana daga cikin wad'anda aka baiwa L.B.A. a 1957 kuma yana da Lasisi na INPORT da EXPORT.