S. Racah 
TARIHINSA A TAKAICE


 
          
S. Raccah mai shekara 72 da haifuwa ya zo nan Kano cikin 1915, ya soma cinikinsa ta hanyar sai wa kawunsa gyada mai suna R. Hassan kafin ya ware nasa cinikin. A lokacin da S. Raccah ya bude ciniki ya maida hankalinsa kan cinikin gyada da fata da turare har zuwa juyin zamani in da yanzu akwai su Kantunan Hajja akwai kanfanoni iri iri inda ake yin abubuwa dabam daban. Kuma duk Labanis da Siriyan wadanda Suka zo Kano babu wanda bai sami taimako daga S. Raccah ba, ko da na kudi ko nasiha. Shi S. Raccah wajen taimako ba sai anyi magana ba tun da shi mutum ne mai taimakon kowa da kowa har ma an ce ya zama TARIHI ne gare shi wajen sha'anin taimako. Kuma ya yi wa 'ya'yansa maza 3 da aka haife su a nan Kano tarbiyya mai kyau da kuma yadda za su zauna ko hulda da jama'a da kuma su taimaki jama'a yadda ya kamata. Ganin sun gogu da kuma daukar duk tarbiyyar da ya gwada musu shi ya san ya ya danka musu duk sha'anunkansu a hannunsu.
               Wannan haton dan FREDERICK GEORGE ne, shi Firjoji ya zo nan Kano tun 1903 kamar yadda kuka gani a cikin tarihin su Alhaji Baba Latsu da Alhaji Hassan na Badamasi da kuma cikin tarihin Alhaji Alhassan'Dantata. Firjoji ya rasu a nan Kano cikin 1961 yana da shekara 84 da haifuwa, ya bar 'ya'ya 8 maza da mace. Shi Firjoji yana daya daga cikin ko kuma na farko da suka bude kanti a waje na kaya iri iri su ne wadanda ke kira da Hausa YUSUFU HALILU KULLUHUN WAWA'UN kuma shi mai haton nan shi ne mai Plaza da Place Cenema na nan Kano daya daga cikin 'ya'yansa.