TAKAITACCEN TARIHIN
 MALAM SALGA


Dukan yabo ya tabba ga Allah, Sarkin da ya tsirad da wanda ya so, daga bayinsa da abin da ya so ya fifita shashinsu bisa shashi, ya sanya sashinsu Sarakuna da shugabanni, shashinsu Malamai, da mawadata, shashi daga garesu KasKatattu, kamar yadda ya fifita shashin sammai bisa sashin Kassai mafificin rahamomi mafi tsarkin gaisuwa su tabbata bisa wanda ya ce, wanda Allah ya ke nufin alheri da shi, ya kan sanar da shi cikin addini. Ya kuma ce, wanda ya wulakanta masanin addini Allah ya wulakanta shi, ko kamar yadda ya fada, Allah ya yi rahama bisa alayansa, da Sahabbansa da Aminci.
Malam Muhammadu Salga dan Alhaji Umarun Jari ne, wani mashahurin attajirin falke da aka haife shi a Salga, wani gari kusa da Kumasi ta Gold Coast da yanzu a ke kira Ghana. Haifuwar dai a 1285 A.D. watau daidai da shekarar 1865 Alhaji Umarun Jari ya haifi Malamin wajen fatauci. Karatun A1kur'aninsa kuwa ga Malam Muhammadu Takiki ya yi shi. A takaice dai sai da ta kai shil da kansa yana karanta Alkur'ani (Mai Girma) tare da rubuta shi da kansa irin yadda Mahaddata su ke yi. Amma shi juyar rubutun ya ke yi yana zuwa makarantar ilmin Arabi ana koyar da shi, bayan ya yi karatun da rana. Cikin dare kuma mahaifiyarsa ta tsare shi da niyyar kiyaye abin da aka koyar da shi.
Wannan kuwa ya faru ne saboda tun daga ranar da aka haife shi, mahaifiyarsa ta dakantar da baki dayan tafiye-tafiye da sanya reno da tarbiyyar danta gareta. Ilmin Fikihunsa dai ga Alhaji Abubakar 'Dan Malam Musa Mai risala da almajirin Malam Kisko na Katsina ne. Bisa gaskiya fa yawancin karatu Malamin daga Karshe a Kano ya yi shi.