TARIHIN ALHAJI IBRAHIM RINGIM 1892.


               TARIHIN ALHAJI IBRAHIM RINGIM, an haife shi cikin 1892 a Ringim kasar Kano. Sunan mahaifinsa Abdur'rahaman, ana ce masa MaiGidan (Kirarinsa wato yabo wanda a ke ma shi MaiGidan akan ce masa Audu mai kudi).

         Shi wannan Dattijo yasa Alhaji Ibrahim a Makarantar Al'kura'ani, wajen Malami ana kiransa Mallam Dauda. Shi Alhaji lbrahin yayi kokari, don haka aka dinga kiransa DAKUNDI.

             Bayan da ya zama mutum sosai, sai ya kama Gadon Tsohonsa, wato Saye da Sayarwa, kamar Haja, Goro, Fata da Gyada, wadda lokacin da Ambirzin sukaje wato suka bude cinikin nasu a Ringim sai wani Manajansu waishi Mr. 'Byland' ya nemi Alhaji Ibrahim ya zama wakilinsu a nan Ringim. Amma sai shi Alhaji Ibrahim yace sai yaje ya shaidawa Mahaifinsa (MaiGidan). Sai Mahaifinsa (Mai-Gidan) yace A-A, sai Alhaji Ibrahim ya Dogara da irin Arzikin da Allah ya yi masa shi Alhaji Ibrahim din). Sai shi Baturen nan ya yi ta rarrashin Mai-Gidan, bar dai shi Mai-Gidan ya yiwa shi Alhaji Ibrahim izini. Ya za- ma Wakilin Amburzin daga 1929-1931.
            Daga nan sai U.A.C. da P.Z. suka nemeshi da cinikidon haka sai ya bar Amburzin yana zaman Kansa. Tun cikin 1932 U.A.C,. P.Z.,.C.F.A.O., G.B.O., duk su yake bawa Gyada da Fata. A cikin 1934 sai G.L. Faizan suka nemeshi da ciniki, suka bashi dama sosai, don haka sai ya amsa. A takaice dai Alhaji Ibrahim Ringim ya zama Gabas da Kano Gumel da Hadeji'a, san nan babu Nguru, don haka har ya zuwa Gaidan duk ciniki yana Hannunsa. Don hakane kowane Kamfani ya kan nemi yayi Zarafi da shi (Alhaji Ibrahim). Kuma Babban Dalili shine Gaskiya a cikin Hurda da Su. Su Kuma jama'a abin da ake basu sha'awa da shi wato saukin Kai da Fara'a, domin wannan zarafi du yana zaune akan Buzu, in ya tasili daga aiki ba Kujera ko wani abu daban ba. Kuma wannan bai sa ya manta da aikin Gona ba a kullum idan Damuna ta Sauka kamar Mutum 150 zuwa 200 suna Gona. In ya sami damar saukin Baki shima yana cikin ‘yan aiki yana yi musu sannu, ya na sa masu Albarka. Wani abin ban sha'awa duk mutanennan shi zai rarraba musu Abinci da Hannunsa, mutum uku-uku, ko Tuwo ko Fura, ana Karshe in an samu mutum biyu shine na cikon uku da shi zasu ci tare. Shine zai dinga kara musu Miya da Kansa. Kuma sau yawa shi zai dauki Kwarya yana yawo yana basu ruwa. Ya sai Motoci biyu, d'aya Doji sabuwa ton biyar (5) a S.C.O.A. don aikace aikacensa a 1935. Ya sayi Fodi Kita a J Allen dan tafiya Mekka shida Malaminsa Alhaji Usman da Dansa Alhaji Uba Ibrahim cikin 1936. Ya tafi Haji ta Mota tare da
Mai Girma Sarkin Katsina A. Mohammadu Dikko, Allah yaji Kansu baki daya. Hakan ku wa ta samu ne saboda hadasu da Mai Girma da Martaba Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya yi, Allah ya yi masa Rahama ya kyauta Bayansa har Abada Amin. To, a taikaice haka wannan Mutum Allah ya yi masa Arziki da Sutura da Zuri'a har zuwa Ranar da Allah ya yi Masa Rasuwa ran 15/5/65. Jana'izarsa akayi ta a Ringim Mi1 44 Gabas da Kano. Mota fiye da 200 taje Ringim don Jana'iza da Ta'aziya, Mallam Atiku shi ya yi masa Sallah, Mal1am Tijjiani usman da Mallam Shehu Mai Hula da Mallam Atiku suka hada shi a AIahdi (wato Kabarinsa), Allah yaji Kansa Shii, Ya Rahamsheshi AMEN.

Alhaji Uba Ibrahim Ringim.

 

Alhaji Uba Ibrahim Ringim an haifeshi 1921 wanda ya shiga harkokin ciniki tare da mahaifinsa tun yana da shekara 22 (1943) bayan ya gama karatunsa na AIkur'ani. shi Alhaji Uba ya komo nan Kano cikin 1958 bayan mahaifinsa ya ga duk ya fahimcin yadda zai yi harkokin ciniki.
A yanzu shi A. Uba yana kan harkokin ciniki dabam daban wanda su ke daidai da zamani inda ya ke yin Import da Export Zuwa Holland, Jamani, Landan da Paris inda yake aikawa da Kaho, Kashi, Citta aho, yana sayo kekunan dinki kaninfari, Sukari, fatun buhu, da yadudduka iri iri na tutafi. Kuma akwai Factories nasa da ke rairaye gyada wadda ya kan aika da ita Holland Jamane da Ingila inda akwai ma'aikata kamar 400-500 maza da mata kuma akwai Kanfanin NPTC. wanda ya ke Manager director wanda da sunan Cop: ya ke rike da L.B.A na Sayen gyad'a tun 1959.